Imam Salihiyyah Tv

Imam  Salihiyyah Tv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Imam Salihiyyah Tv, Restaurant, Minna.

DA DUMI-DUMI: ’YA’YAN SHEIKH MAKKY SUN YI GODIYA GA KHALIFA SHEIKH IBRAHIM DAHIRU USMAN BAUCHI’Ya’yan marigayi Sheikh Ma...
03/09/2026

DA DUMI-DUMI: ’YA’YAN SHEIKH MAKKY SUN YI GODIYA GA KHALIFA SHEIKH IBRAHIM DAHIRU USMAN BAUCHI

’Ya’yan marigayi Sheikh Makky sun miƙa godiyarsu ga Khalifa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi, bisa irin ƙoƙari da gudunmawar da ya bayar wajen taimaka musu a lokacin da suke cikin wani hali na rashin mahaifinsu.

A cewar bayanan da aka samu, Khalifa Sheikh Ibrahim ya ɗauki nauyin sayen tikitin jirgi kai tsaye, tare da jagorantar aikin ɗauko gawar mahaifinsu daga ƙasar Morocco zuwa Senegal domin a kai ta ƙasar haihuwarsa.

’Ya’yan Sheikh Makky sun bayyana jin daɗinsu da godiya bisa wannan mataki, wanda s**a ce ya nuna tausayi, zumunci da kulawa a lokacin da suke cikin babban rashi.

Sun kuma roƙi Allah Ya saka wa Khalifa Sheikh Ibrahim da alheri, Ya ƙara masa lafiya da ƙarfi, Ya kuma karɓi wannan hidima da ya yi.

Muna roƙon Allah Ya jiƙan Sheikh Makky, Ya gafarta masa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya bai wa iyalansa da ɗaukacin masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.

Rahoto: Usman Zun'Nurain

🕊️ SANARWA TA MUSAMMAN GAME DA SALLAR JANA’IZAR MARIGAYI 🕊️SHEIKH MOUHAMED EL MEKKI IBRAHIM NIAYSS (R.A.)INNĀ LILLĀHI WA...
03/09/2026

🕊️ SANARWA TA MUSAMMAN GAME DA SALLAR JANA’IZAR MARIGAYI 🕊️

SHEIKH MOUHAMED EL MEKKI IBRAHIM NIAYSS (R.A.)

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJI‘ŪN

Khalifa Sheikh Muhammadul Mahi Sheikh Ibrahim Niass (R.T.A.) na sanar da ɗaukacin ’yan uwa, masoya, almajirai da sauran al’ummar Musulmi cewa, in shā Allah, za a gudanar da Sallar Jana’izar Marigayi Sheikh Mouhamed El Mekki Ibrahim Niass (R.A.) bayan Sallar Juma’a.

🕌 WURI: Babbar Masallacin Maulana Sheikh Ibrahim Niass, Madinatu Kaulakh
📅 RANA: Juma’a, 4 ga Satumba, 2026
⏰ LOKACI: Bayan Sallar Juma’a

Haka nan, ana kira ga kowa da kowa da ya kiyaye tare da bin dukkan shirye-shiryen da aka tanada domin gudanar da Sallar Jana’izar cikin tsari, lumana da haɗin kai.

🤲 ADDU’A

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya lullube Marigayi Sheikh Mouhamed El Mekki Ibrahim Niass (R.A.) da rahamarSa marar iyaka, Ya gafarta masa zunubansa, Ya haskaka kabarinsa, Ya ɗaukaka darajarsa zuwa mafi girman matsayi a Aljannatul Firdausi.

Allah Ya saka masa da mafificin alheri bisa irin gudummawar da ya bayar wajen hidimtawa Musulunci, Ɗariƙar Tijjaniyya da Faidha, Ya kuma sanya dukkan ayyukansa na alheri su zama sadaka jariya a gare shi.

Allah Ya haɗa mu da shi cikin rahama da falalarSa, ƙarƙashin tutar Shugabanmu Annabi Muhammadu ﷺ.

ĀMĪN, SUMMA ĀMĪN. 🤲🏽🖤

✍️ Usman Zun’Nurain

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJIʿŪN. 😭Cikin alhini da jimami, an samu labarin rasuwar Sheikh Muhammadul Makky, ɗan Sheik...
01/09/2026

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJIʿŪN. 😭

Cikin alhini da jimami, an samu labarin rasuwar Sheikh Muhammadul Makky, ɗan Sheikh Ibrahim Niass (RTA).

Wannan babban rashi ne ga iyalai, ’yan uwa, ɗalibai da kuma masu ƙaunar Shehu Ibrahim Niass (RTA).

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa, Ya haskaka kabarinsa, Ya ɗaukaka darajarsa, Ya sanya Aljannar Firdausi ce makomarsa.

Allah Ya ba iyalansa, ’yan uwansa, ɗalibansa da daukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi, Ya maye musu da alheri.

Rahoto: Imam Salihiyyah TV

Allah Ya Kara Maku Lfy Maulana Alfarman Shugaban Halita ( S.A.W )🥰🥰🥰🥰🥰
28/08/2026

Allah Ya Kara Maku Lfy Maulana Alfarman Shugaban Halita ( S.A.W )
🥰🥰🥰🥰🥰

📻🎙️ IMAM SALIHIYYAH ONLINE RADIO (1447H/2026M) – A Garin Minna 🎙️📻📚 Karatun Ranar Laraba📍 Wuri: Mu'assasatu Maulana Shei...
20/08/2026

📻🎙️ IMAM SALIHIYYAH ONLINE RADIO (1447H/2026M) – A Garin Minna 🎙️📻

📚 Karatun Ranar Laraba

📍 Wuri: Mu'assasatu Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation, Minna Branch, Fadukawi, Kutirko, Niger State.

🎤 Zama Na 09

📚 A Cikin Littattafan: 1️⃣ Al-Akhdari 2️⃣ Arba'una Hadith 3️⃣ Ta'alim

🎙️ Mai Gabatarwa: Maulana Sheikh Imam Umar Assalihee (R.T.A.) – Nigeria

🎧 A Yi Sauraro Lafiya.

🤲 Addu'a: Allah Ya sanya albarka a cikin wannan karatu, Ya sa ya zama sanadin ƙaruwa da ilimi, fahimta, da aiki da abin da aka koya. Allah Ya amfanar da al'umma baki ɗaya da wannan majalisi mai albarka. Amin Ya Rabbal 'Alamin.

📻 Imam Salihiyyah TV

Barka da Watan Maulidi 💖🌙Muna ƙara taya ku murna da zagayowar watan farin ciki da murna, watan godiya, watan soyayya da ...
17/08/2026

Barka da Watan Maulidi 💖🌙

Muna ƙara taya ku murna da zagayowar watan farin ciki da murna, watan godiya, watan soyayya da ƙaunar Manzon Allah ﷺ. 💖💝🌙

Allah Ya sanya wannan wata mai albarka ya kasance mana sanadin ƙara ƙaunar Sayyidina Muhammad ﷺ, yawaita salati da sallama gare Shi, da samun albarka da rahama a rayuwarmu. 🤲🏽❤️

🌹 اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا محمد ﷺ 🌹

Muna taya al’ummar Musulmi baki ɗaya murnar shigowar wannan wata mai albarka.

✍️ Imam Salihiyyah TV

Saƙon Taya Murna Ga Sabon KhalifaALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! 🌹✨Da matuƙar farin ciki da godiya ga Allah...
14/08/2026

Saƙon Taya Murna Ga Sabon Khalifa

ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! 🌹✨

Da matuƙar farin ciki da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, muna miƙa saƙon taya murna da fatan alheri ga babban bawan Allah, Khalifa Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A.), bisa wannan babban matsayi da aka ƙara ɗora masa.

A yammacin yau, bayan kammala Zikirin Juma’a, Wazifa da Sallar Isha’i, Sheikh Muhammadul-Mahy Niass ya nada Khalifa Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A.) a matsayin Khalifansa a Najeriya, tare da ƙara jaddada masa matsayin Khalifancin Lisanul-Faidhati.

Wannan babban nadi ba ƙaramin matsayi ba ne, kuma ya zo ne bisa irin jajircewa, sadaukarwa da tsayin daka da Khalifa ya nuna wajen ci gaba da ayyukan da Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A.) ya assasa, tare da hidimtawa ga Ahalin Shehu Ibrahim Inyass (R.T.A.) da kuma Ahalin Shehu Tijjani (R.T.A.).

Muna addu’a Allah Ya ƙara wa Baba Khalifa lafiya, hikima, ƙarfi da ikon sauke wannan babban nauyi da aka ɗora masa. Allah Ya taimake shi wajen cika wannan amanar, Ya sanya wannan khalifanci ya zama sanadin haɗin kan Ahlul-Faida, ƙara yaɗuwar koyarwar Shehu Tijjani (R.T.A.), da samun ƙarin albarka da ci gaba.

Allah Ya taya ka riƙo, Baba Khalifa. 🤲🌹
Allah Ya ba ka ikon ɗaukar nauyin wannan amanar da aka ba ka, Ya ƙara maka daraja da matsayi, Ya kuma sa mu ga alherin wannan nadi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

14/08/2026

Saƙon Taya Murna Ga Sabon Khalifa

ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! 🌹✨

Da matuƙar farin ciki da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, muna miƙa saƙon taya murna da fatan alheri ga babban bawan Allah, Khalifa Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A.), bisa wannan babban matsayi da aka ƙara ɗora masa.

A yammacin yau, bayan kammala Zikirin Juma’a, Wazifa da Sallar Isha’i, Sheikh Muhammadul-Mahy Niass ya nada Khalifa Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A.) a matsayin Khalifansa a Najeriya, tare da ƙara jaddada masa matsayin Khalifancin Lisanul-Faidhati.

Wannan babban nadi ba ƙaramin matsayi ba ne, kuma ya zo ne bisa irin jajircewa, sadaukarwa da tsayin daka da Khalifa ya nuna wajen ci gaba da ayyukan da Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A.) ya assasa, tare da hidimtawa ga Ahalin Shehu Ibrahim Inyass (R.T.A.) da kuma Ahalin Shehu Tijjani (R.T.A.).

Muna addu’a Allah Ya ƙara wa Baba Khalifa lafiya, hikima, ƙarfi da ikon sauke wannan babban nauyi da aka ɗora masa. Allah Ya taimake shi wajen cika wannan amanar, Ya sanya wannan khalifanci ya zama sanadin haɗin kan Ahlul-Faida, ƙara yaɗuwar koyarwar Shehu Tijjani (R.T.A.), da samun ƙarin albarka da ci gaba.

Allah Ya taya ka riƙo, Baba Khalifa. 🤲🌹
Allah Ya ba ka ikon ɗaukar nauyin wannan amanar da aka ba ka, Ya ƙara maka daraja da matsayi, Ya kuma sa mu ga alherin wannan nadi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

🌙✨ YANDA AKA GUDANAR DA TARON ZIKIRIN JUMA’A ✨🌙Alhamdulillahi Rabbil ‘Alamin! 🤲❤️Cikin ikon Allah, an gudanar da Babban ...
14/08/2026

🌙✨ YANDA AKA GUDANAR DA TARON ZIKIRIN JUMA’A ✨🌙

Alhamdulillahi Rabbil ‘Alamin! 🤲❤️

Cikin ikon Allah, an gudanar da Babban Taron Zikirin Juma’a cikin nasara da ɗaukaka, tare da halartar Manyan Khalifofin Ɗariƙar Tijjaniyya daga sassa daban-daban na duniya, a Babban Masallacin Maulana Sheikh Dahiru Bauchi (R.T.A.) da ke Central Market, Bauchi.

Taron ya kasance cikin yanayi mai cike da zikiri, salati ga Manzon Allah ﷺ, karatun Alƙur’ani, addu’o’i da wa’azi, inda dimbin al’umma s**a hallara domin neman kusanci da Allah Maɗaukakin Sarki da kuma ƙara soyayya ga Manzon Allah ﷺ. 🌹🕌

Wannan babban taro ya sake nuna irin muhimmancin Zikiri, haɗin kai da zumunci tsakanin Ahlul-Faidha da masoyan Ɗariƙar Tijjaniyya daga sassa daban-daban na duniya.

🤲 Allah Ya karɓi zikiranmu, Ya amshi addu’o’inmu, Ya ƙara mana soyayya ga Manzon Allah ﷺ, Ya tsare manyan Khalifofinmu da dukkan Ahlul-Faidha.

🌹 اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا محمد ﷺ 🌹

📍 Babban Masallacin Maulana Sheikh Dahiru Bauchi (R.T.A.)
📍 Central Market, Bauchi

Alhamdulillah Ala Ni’amatil Islam 🤲❤️
Zikiri — Soyayya — Zumunci — Faidha 🌙🌹

🌙❤️ HAPPY MAULIDUN NABI ﷺ ❤️🌙✨ أهلاً بشهر المولد شهر الأولى وسؤدد شهر النبي أحمد شهر الربيع الأول 🌙🌹🌹 اللهم صل وسلم وبار...
13/08/2026

🌙❤️ HAPPY MAULIDUN NABI ﷺ ❤️🌙

✨ أهلاً بشهر المولد شهر الأولى وسؤدد شهر النبي أحمد شهر الربيع الأول 🌙🌹

🌹 اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا محمد ﷺ 🌹

🎉 HAPPY MAULIDUN NABI ﷺ 🎉

Maulana Sheikh Imam Umar Assalihee (R.T.A.) ✍️

Zunnurain Graphics

Address

Minna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam Salihiyyah Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Imam Salihiyyah Tv:

Shortcuts

Share

Category