14/01/2024
Masha Allah da wannan gwabna Allah ya kara masa lafiya da Nisan kwana🙏
Kwankwaso, Shekarau da Ganduje sun samu gurbi a gwamnatin Abba Gida Gida
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kafa Zauren Dattawan Kano domin karɓar shawarwarin da za'a ciyar da Kano gaba, wanda aka sanya tsofaffin gwamnonin Kano a cikinsa, da tsofaffin mataimakan gwamna, tsofaffin shugabannin majalisar Dattijai da wakilai da ta dokokin jihar Kano.
Daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne bayyana haka ga manema labarai a ranar Asabar, inda yace an kafa Zauren ne domin karɓar shawarwarin da za'a ciyar da Kano gaba, kasancewar mambobin Zauren sun riƙe kujerun iko daban-daban, su na da gogewa da sanin yadda al'amura ke gudana.
Ragowar mambobin Zauren sun hada da tsofaffin sakatarorin gwamnatin Kano, tsofaffin Alƙalan kotun ƙoli, kotun ɗaukaka ƙara da babbar kotun jiha, sai kuma tsofaffin shugabannin ma'aikata, wadanda s**a kasance dukkansu yan asalin jihar Kano ne.
Hakazalika sanarwar ta bayyana cewa, a cikin Zauren akwai shugabannin malamai na Addini, sarakunan gargajiya, yan Kasuwa, tsofaffin shugabannin bangarorin tsaro da sauran manyan muhimman Mutane da gwamnan ya nada.
14/1/2024