29/06/2026
Haka Ahlulbait (as) s**a koya mana kuma shi zamuyi ko ya sabawa wasu. !!! Idan muje lahira bayansu zamu boye kai kuma ka tafi wajen maliku da shafi'i da hanbali.
-
WASU MAS'ALOLI DA YA KAMATA MUSANI A MAKARANTAR AHLULBAITI (AS)
-
1) Idan inabin liman sallah Raka'oin buyun karshe, zakayi karatun fatiha. Ba shiru zakai ba.
-
2) Abinda ake nifi da boye karatu a sallah. Shine yadda na kusa dakai bayajin abinda kake cewa. Ba wai karatun zuci ake nufi ba.
-
3) dole kayi wankan janaba ko kiyi wankan tsarki kafin alfijir ya fito idan zakuyi azumi. Idan jini ya dauke kafin alfijir kuma kece baki duba ba sai kin rama azumin ranar.
-
4) mace mai shayarwa ko junabiyu idan batai azumi ba zata rama kuma zata fidda mudu na abinci kowace rana.
-
5) Tsoho da tsohuwa da masu rashin lafiya ta Kishirwa, zasu aje azumi amma zasu fidda mudu na abinci ba sai sun rama ba.
-
6) Ruwan da yake saukar ma mace (Ni'ima) idan sha'awa mai karfi ne yasa ya fita, ko miji bai kusanceta ba, sai tayi wanka.
-
7) wajibi ne wanda zaiyi tafiyar da takai Kasaru, ya aje azumi. Idan ma yayishi sai ya rama shi. Saidai idan yanaso yayi azumin, yabar tafiyar sai bayan zawali.
-
8) Idan mace ta haihu jini bai tsaya ba har kwana 10 to zata cigaba da azuminta da sallah tanayin wanka. Amma idan ranar haihuwar ya dauke to zata fara sallah daga ranar.
-
9) lokacin buda baki shine idan jajatan gabas ya bace, alamun rana ta fadi kenan.
-
10) Saki baya inganta sai idan mace tana cikin tsarkin da mijin bai taketa ba. Kuma yazama gaban adilai guda 2 kuma da larabci, idan mijin ya iya.
-
11) Idan kayi sallar juma'a ba sai kayi wata zuhurba, ko a masallacin Sunnah kayi sallar indai ta cika sharudda.
-
12) Wanda yayi mafarki yana azumi har maniy ya fita, azuminsa bai kare ba, zaiyi wanka ne kawai. Sannan maniy najasa ne. Duk Inda ya taba wajibi ne a wanke gurin.
-
Allah ya bamu ikon aiki da abinda iyalan annabi (saw) s**a koyar daga annabi.
-
Khadim Arkam A/Hadi Abu Ashtar (Al'ha'iriy)
Hauzatul Qa'im (AF) Tanbaya da amsa